Bag om Muhimmancin Addu'a
Tun Adamau da Hawwa'u zuwa ga Manzo Yohanna, ana samun addu'a duk cikin Maganan Allah. Yawancin mu mun san addu'a na da muhimmanci, amma sai mu samu kanmu muna gwagwarmaya da sa shi na farko a cikin rayuwan mu na kullum
Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jin¿ai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari. Ibraniyawa 4:16
Cikin addu'a, akan gayyace mu mu samu zumunci da Allah yayinda mu ke kusance Shi, muna amincewa da sanin mu na bukatan kasancewan Shi a cikin rayuwan mu
Amma duk da wannan sani, dayawa daga cikin mu na gwagwarmaya da yin amfani da wannan zarafi. Cikin rashin sanin mu, sai mu na yi kamar mu na da karfin kawas da jaraba, ko mu na da karfin yaki da harin shai¿an, ko mu na da wayo sosai da za mu iya samun hanyan mu da kan mu cikin wannan duniya, ku mu na da ilimi sosai da za mu iya gane ma'anar Maganar Allah da kan mu. Allah bai so mu yi rayuwa haka ba.
Idan ki na bukatan ki kusanci Mai Ceton ki ta wurin sa addu'a ya zama babban muhimmanci a rayuwan ki, to Muhimmancin Addu'a an yi ne domin ki. A cikin wannan binciken Littafi mai Tsarki na tsawon mako shida daga Love God Greatly, za mu ¿auki lokaci cikin Maganan Allah, za mu nemi amsoshi ga tambayoyi game da yadda yakamata mu yi addu'a, da yadda zamu sa addu'a ya zama da muhimmanci, da kuma ko Allah Ya na ji ko ba Ya jin addu'o'in mu. Mu yi bincike tare yayinda mu ke shiga cikin Maganan Allah, cikin karatu da rubuta abin da Allah ke fäa wa zuciyar mu.
Mu na begen za ki häa kai da mu a yanan gizo domin wannan binciken Littafi mai Tsarki na tsawon mako shida ko kan app namu na Love God Greatly. Za ki samu abubuwan da ya shafi Muhimmancin Addu'a a duka wurare biyu tare da rubuce rubucen mu na Litinin, Laraba da Jumma'a, kari bayani ta wurin karatu na kullum da kuma jama'a masu kauna domin su yi tafiya da ke yayinda ki ke binciken muhimmancin addu'a!
Vis mere